Ticker

6/recent/ticker-posts

TAYAYA SUKA MUSULUNTA!?

 TAYAYA SUKA MUSULUNTA BAYAN SUN KASANCE WADANDA KE NUNAWA MUSULUNCI KIYAYYA A TURAI.



Sun kasance masu nuna kiyayya matuka ga musulunci da mususlmai amma yau an wayi gari suna masu kareshi da soyayya, 

ALLAHU AKBAR 


1- warner clown: ya kasan ce dan kasar germany kume me nuna kiyayya ga yan gudun hijiria, da musulunci, da musulmai, kuma shi member ne na wata jam'iya me nuna adawa ga musulunci da musulmai da kuma yan gugun hijira, me suna 'NEO NAZI'

Bayan komawarsa musulunci ya maida sunan shi ibrahim, ya kasance kuma yana nunawa yan gudun hijira soyayya, wanda har ya karbi yan gudun hijira guda hudu suke rayuwa a gidansa,

   Bayan ya musulunta ya shedawa gidan jaridar Bild ta jamus cewa  ya karanta wani mawaki me suna johann wolfgang wanda ya shahara da kwamandan harshen larabci,

Kuma ibrahim kafin ya MUSULUNTA ya kasance yana karanta waqoqin johnn wolfgang na yabon manzon ALLAH (s.a.w) sannan ya karanta Al-qur'ani me girma har zuciyar ta bude ya karbi addinin musulunci, kuma yaje makkah ya gudanar da aikin hajji, yace yanzu yana zaune lafiya,

ALLAHU AKBAR


2- Arthur wagner: ya kasance kafin musulunci kirista me ra ayin mazan jiya, kuma arthur wagner memba ne na cocin furotesta kuma shine shugaban wata kungiya me suna ( alternativ for germany ) wannan jam'iyya tana adawa da musulunci da musulmai.



  A shekarar 2018 january arthur wagner ya bayyana ya koma musulunci, kuma ya bayyana a wasu shahararrun tashoshin jamus yana me kare addinin musulunci, kuma yana bude Qur'ani ya karanta tafsirin sa kai tsaye, kuma ya bayyana cewa ze je ya koyi larabci domin ya dinga karanta Al-qur'ani me girma 


3- Arnaud van doorn: dan kasar holland ne kafin ya musulunta ya kasance shine darakta na GEERT WILDERS kuma yanzu  geert wilders shine kan gaba wajan yaki da musulunci a turai, an san arnaud a matsayin furodusa na wani fim da bai dace ba a 2008, yada wannan fim ya fusata duniyar musulunci, bayan musuluntar sa, ya wallafa wani rubutu a shafin sa na twitter ( shaida biyu ) yayi rubutun aka tabbatar musuluntar shi dakuma labarin yadda ya musulunta kamar wani zuwan Waliqiya ne



Bayan ya musulunta ya kasance yana nuna goyon bayan manufofin musulunci da karfin gwiwa, kuma ya jagoranci jam'iyyar UNITY PARTY ( shugabancin musulunci )

Shi kadaine aka taba nadashi a matsayin shugaban kungiyar, 

Ya tuba a gameda abinda yayiwa manzon ALLAH (s.a.w) kuma ya bawa musulmai hakuri kuma ya nemi afuwar su a kan abinda yayi na temakawa wajen yada wannan fim da baidace ba a 2008. Shekara daya da musuluntar shi babban dansa ya biyo bayan shima ya musulunta.

ALLAHU AKBAR


4- JORAM VAN KLAVEREN: wannan bawan ALLAH dan kasar hollanda ne, kuma shine mawallafin maganar  " ISLAMIC IS LIE AND QUR'AN IS POISON" yace Musulunci Qarya ne Qur'ani kuma guba ne .



Shine na hannun daman geert wilders shugaban kungiyar pvv kungiyar da ke kyamar  musulunci

   Joram van klaveren ya fito daga zuriyar kiristoci masu ra'ayin mazan jiya, ya tsani komai na musulunci, ya bada shawarar hana saka hijabi da kuma hana gina manarar masallaci, kuma ya jagoranci yaki me zafi da  musulunci a majalisar dokokin holland,

Sunan shi ya kasance tareda na babban makiyin musulunci geert wilders,

Kwatsam a 2018 ya sanar da musuluntar shi,

Gidan jaridar NRC ta rawaito shi yana cewa yana shirya wani littafi da ze kushe musulunci amma yanzu ya juya Ra'ayin kuma ya juya littafinsa zuwa " hujja don karyata ra'ayin wadanda ba musulmi ba"

Ya sanar da musuluntar sa kuma ya yayi magana akan matsayin mata a musulunci kuma ya kare manufar musulunci ta cewa a auri mace sama da guda 1 daya,

A tattaunawar shi da dutch rediyo yace " Ra ayina gameda musulunci me rauni ne kuma da tsoro.

inda yake kare musulunci kuma yana kira zuwa ga a fahimce shi, littafin nashi ya zama sananne, kuma an bugashi a shekarar 2019.

 Daga shekarar 2018 zuwa 2022 joram van klaveren ya fuskanci barazanar kisa  sau dubu biyu akan ya musulunta kuma yana kare musulunci kuma yana wankeshi daga tuhumar kafirai.

ALLAHU AKBAR.


Allah ya karawa musulunci daukaka, su kuma ALLAH ya karesu daga sharrin masu sharri ameen


Post a Comment

0 Comments