Ticker

6/recent/ticker-posts

YADDA AKE MAIDA COCI MASALLACI A TURAI

Yadda ake maida coci masallaci a turai


Mun sani cewa yawancin turawa ba musalmai bane amma wani abun mamaki shine musulunci yana kara burunqasa a turai inda har ana maida coci masallaci,

Wasu daga cikin yankunan da akafi samun juya coci zuwa masallaci da kuma samun yawan musulunta sune BRITISH, CANADA, AUSTRALIA dakuma U,S,A 

 daga yanzu zuwa shekaru ashirin da uku da suka wuce a kasar CANADA, coci sama da ashirin an maida su masallatai a iya kasar CANADA banda sauran kasashen, mazauna kasar CANADA suna tunanin wannan a matsayin kafuwar musulunci a turai

a kasar TURKEY akwai wata coci babba kuma me tarihi kafin a maida ita masallaci ana kiranta da CHURCH OF WISDOM , 

fiye da shekaru duba da suka wuce wannan cocin takasance babu coci me girma a duniya kamarta kuma itace wurin tarihin mutanen lokacin, amma lokacin daular usmaniyya sarkin wannan lokacin ya maida wannan coci masallaci a shekarar 1435, se dai an

maida wannan masallacin Gidan tarihin kasar turkiya a shekarar 1935, ana nan tafe wannan gini me tarihi, shugaban kasar turkiya Erdogan ya sake maida shi masallaci a shekarar 2020, har yanzu yana nan a matsayin masallaci kuma muna sa ran ze tabbata a masallaci in sha Allah


WEMBLEY CENTRAL MOSQUE: wannan masallacin ya kasance asalin ginin coci ne a garin london a shekarar 1904 har zuwa 1993


 shekarar da musulmai suka siye wannan masallacin, cocin ta shafe shekaru 15 ba masu zuwa,  se musulmai sukayi wuf suka siye cocin suka maidata masallaci hakan ya kawo samun musuluntar mutane da yawa a garin har zuwa yanzu ana samun karuwar hakan, 

musulmai sun karawa ginin girma sosai kuma an bude makaranta a ciki da wurin wake mamaci da sauran wurare na musulunci, babban malamin nan kuma makarancin Al qur'ani sheikh Abu bakr Shatri ya taba ziyartar masallacin.

JAMI MOSQUE CANADA: a shekarar 1910 aka gina cocin me suna presbyterian church,

 musulmai sun sayi wannan cocin a shekarar 1969 kuma suka maida cocin masallaci, inda wannan masallacin ya zama masallaci na farko a garin toronto,


MASJID NOOR-UL-ISLAM:  a shekarar 2012 musulmin unguwar windsor suka siye cocin dake kan titin lincoln road,

wannan coci ta kasance tsohuwar coci me tarihi, se dai abin al faharin mu shine yanzu wannan gini an gyara shi kuma an maida shi masallaci kuma ana karantarwa a ciki, ginin ya kai shekara 100 a hannun kiristoci musulmai su mallake shi a shekarar 2012, daga maida wannan coci masallaci anata samun musuluntar kiristoci a garin da kuma kasar, har wasu sassa na gefen kasar suna ta musulunta, 

Kirista sun nuna rashin jin dadin su akan wannan Al amari 


CHATHAM ISLAMIC CENTER: wannan kungiya a shekarar 2021 suka mallaki wata coci me suna st james,

kuma suka maida ita masallaci kuma cibiyar wannan kungiya, duba da yadda ake samun karuwar adadin masu musulunta wannan ya sanya wannan kungiya siyan wannan gini na cocin st james,

Zuwa yanzu 2023 akwai musulmai dubu kan dubu a garin chatham a kasar canada.

AL NOUR MOSQUE HAMBOURG:  a shekarar 2012 wata coci a kasar germany, musulmai suka saye ta kuma suka maida cocin masallaci,



hakika wannan babbar nasara domin cocin babbar coci ce, amma yanzu tana gudana a matsayin masallaci me daukan masallata sama da 2000 

Idan mukayi duba a shekarar 2019 akwai wata tsohuwar coci a garin surrey a kasar canada, an gina cocin a shekarar 1947 amma musulmai sun mallakeshi a 2019 suka maida cocin masallaci, 
Hakika musulunci yana samun karfi a kasashen yamma ( europe ) ta ko ina ana samun musuluntar mutane a kasashe daban daban musamman germany, canada, u.s.a, da sauransu, 
Muna rokon Allah ya temaki musulmai a duk inda suke kuma ya yi mana Albarka 
Ameen


Post a Comment

0 Comments